CIKI DA GASKIYA: An Gama Binciken kwa-kwaf kan DCP Abb Kyari amma ba a same shi da Laifi ba ko daya

CIKI DA GASKIYA: An Gama Binciken kwa-kwaf kan DCP Abb Kyari amma ba a same shi da Laifi ba ko daya

‘Yan nageriya karku aminta kuyi Watsi Da Labarin Karya kan DCP Abba Kyari da Hukumar ‘Yan Sanda da Babban Lauyan Tarayya Abubakar Malami SAN da ‘Yan sandan Najeriya, wadanda kafafen yada labarai irin su Sahara reporter People gazette da Punch da sauran su zuwa masu rubutun ra’ayin yanar gizo ke yadawa wanda wasu Makiya Najeriya ke daukar nauyinsu.

Ta hanyar Rubutacciyar wasikar hukumar ‘yan sanda ta ce, daga dukkan binciken da aka yi da kuma bayanan da suka bayyana ba a gano Dcp Abba Kyari bai aikata wani laifin da zai sa a yi shari’ar zuwa Kotu ba domin haka har yanzu suna bukatar karin shaida da karin bincike daga ‘yan sanda nan da Sati 2 masu zuwa. makonni kafin su tabbatar da Laifin da suke Zargi ko kuma laifin da Abba kyari ya yi wanda Hakan na kan gudana.

An gudanar da cikakken bincike, an duba dukkan asusu na banki kuma babu ko sisi da aka alakanta Abba Kyari kai tsaye ko a fakaice. An gayyaci duk wadanda ke da alaka da lamarin da sauran masu alaka da wannan lamarin kuma an bincika su amma har yanzu babu wata hujja da ke da alaka da Kyari. Wasu da dama sun ce masu bincike sun ji cewa kwamitin ‘yan sanda ya binciki lamarin domin samun shaidun da ake tuhumar Kyari amma har yanzu ba a sami Kyari yana yunkurin aikata wani laifi ba ko kuma ya karbi wani kwabo daya daga hannun kowa ba amma wasu laifuffukan da suka shafi aikin ‘yan sanda na cikin gida kamar karbar korafi tare da fara Bincike ba tare da Amincewa ko sani daga Shugaban Hukumar ‘yan Sanda IGP ba Kokarin kare Kansa da dogaro da kansa a Social Media ba tare da yardar Hukumar Yan sanda ba IGP ba, sune ake Zargin cewa Abba Kyari Yayi kuskure.

- Advertisement -

Mutumin da ya karbi sashin Sako na Viral Media kan Naira miliyan 8 ya shaida a gaban kwamitin ‘yan sanda kuma ya bayar da sanarwar da ta wanke Abba Kyari gaba daya. Ya bayyana cewa shi da kansa ya tattauna Kuma ya aika da bayanan asusunsa sannan ya karbi kudi har miliyan 5 a ranar 4/4/2020 da miliyan 3 a ranar 9/4/2020 domin siyan wasu kaya ga Morgan da ke Dubai ba tare da sanin Abba Kyari ba. Ya kara da cewa bayan sati 6 a ranar 20/5/2020 bayan sun samu sabani da Morgan, Morgan ya kai rahotonsa ga Abba Kyari ta hannun Hushpuppi tunda Morgan bashi da lambar wayar Abba Kyari a wancan lokacin kuma ya aika musu da takardar shedar cinikin 5m da 3m. zuwa ga Abba Kyari ta hannun Hushpuppi a matsayin shaida na shari’ar da ya ke yi wa mai asusun ajiyar. Mai asusun ya ce ya yi mu’amala da Morgan ba Hushpuppi ba kuma sune kudin da kafafen yada labarai ke yadawa na Morgan ne ba Hushpuppi ba. Ya ci gaba da bayyana a gaban kwamitin yana cewa ya yi mamakin yadda FBI da ‘yan jarida ke kokarin alakanta mu’amalar sa da Morgan da Abba Kyari, ya kuma ce ta yaya wannan kudi da Morgan ya aike masa domin sayo wa Morgan Kayya a ranar 4/ 4/2020 kuma rahoto ya kai ga Abba Kyari a ranar 20/5/2020 har ake tuhumar sa da kama Kyari da aka yi watanni 5 a farkon Janairu 2020? An duba dukkan asusu na wannan mutumin da ya karbi miliyan 8 sannan aka samu bayanan asusu, kwamitin ya ga yadda ya karbi Naira miliyan 8 ya kashe a cikin sati 1 a watan Afrilun 2020, ba tare da bai wa Abba Kyari ko sisi ba daya ba kamar yadda bayanin asusun bankinsa ya nuna. da kuma rubutaccen bayanin sa a gaban kwamitin. Duk mutanen da ya yi mu’amala da su na Naira miliyan 8, an gayyace su kuma babu wanda ke da alaka da Abba Kyari ko kuma ya bai wa Abba Kyari ko kwabo.

Haka kuma alkawarin da Hushpuppi da kan sa ya yi a cikin watan Janairu na mayar wa ‘yan sandan da suka je jahohi 4 kudaden da suka kashe a lokacin da suka je kama Vincent kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da Kyari, an yi bincike sosai kuma an tabbatar da cewa ba sami ko kwabo daya da Hushpuppi ya aike da shi ba. Cikakkun bayanan asusun banki da aka samu daga Zenith da bayanin mai asusun da aka rubuta a kwamitin bincike ya fito fili a kan haka.

An kuma kama da binciken Vincent Kelly tare da umarnin kotu na makonni 4 da kotu a Najeriya ta bayar, inda ta ba da izini ga tawagar ‘yan sanda ta tsare tare da bincikar Vincent Kelly akan laifuka sama da 20 na intanet wanda ya amsa laifinsa da Hushpuppi da sauran kungiyoyin ‘yan sanda Malaysia, Cyprus da Afirka ta Kudu.

Kyari ya bayyana cewa duk wata tattaunawa ta Whatssameeda ake yadawa ga manema labarai wani bangare ne na bincike domin sanin ayyukan Hushpuppi, mambobin kungiyarsa da kuma kai shi Najeriya tun bayan kama Vincent sun fallasa laifukan da ya aikata.

An kuma gano cewa Kyari ya san Hushpuppi na tsawon watanni 9, daga Satumba 2019 zuwa Yuni 2020 lokacin da aka kama shi. Har ila yau, ba a gano wata shaida ta hannun Kyari cikin laifukan Hushpuppi ba, Babu wata bukata da Kyari ya taba nema ga Hushpuppi babu wata tattaunawa ta kowane irin kudi ko wani laifi da aka yi tsakanin Kyari da Hushpuppi. Babu wani sisin Naira da Kyari ya taɓa karba daga Hushpuppi kamar yadda bayanai da bincike suka nuna kuma sun tabbata a fili. Idan da FBI ta tuntubi Najeriya da sun yi hira da mai asusun da ya karbi Naira miliyan 8 don gano duk wata alaka da Kyari ko kuma su ji ta bakin Kyari da ya taimaka a lokuta da dama na sace-sacen mutane da kashe-kashen da suka shafi Amurkawa a Najeriya wanda har ma aka bai wa Kyari wasika na lambar yabo daga FBI a cikin 2018.

Hushpuppi ya bukaci Kyari ya daure Vincent ne ta hanyar amfani da laifin fashi da makami Mai daukar mutun tsawon shekaru a gidan yari kamar yadda aka gani a hirar da Hushpuppi ya yi da Kyari yayin da Kyari ke wasa cikin raha da Hikima tare da Hushpuppi domin samun karin bayani game da ayyukansa da kuma kai shi Najeriya ba tare da Hushpuppi ya yi zargin cewa ana bincikarsa shi da Vincent ba karkashin bincike. Kyari cikin hikima ya bayar da belin Vincent a kan matsalar Rashin lafiya ba tare da Jin Fadi Hushpuppi ba wanda Hakan ya sabawa ra’ayin son shi saboda Kyari ya dage cewa Vincent ba shi da lafiya. Idan Kyari zai bi abin da Hushpuppi ke so, ko kuma ya tsaya bayan Kuɗi, da Vincent ya bi Haqqinsa na jinyar ƙaramar rashin lafiyarsa da kuma kunga an tuhume shi da laifin fashi da makami a kotu kamar yadda Hushpuppi ya so a tattaunawar sa ta WhatsApp da Kyari. Wannan ya bayyana dalilin da ya sa Hushpuppi ya yanke shawarar cewa ba zai biya Kudaden da tawagar ‘yan sandan tayi anfani dasu ta kama Vincent ba.

An gabatar da Kyari ga Hushpuppi a Dubai kamar yadda aka gabatar da wasu fitattun ‘yan siyasar Najeriya, ‘yan kasuwa, mashahuran mutane ga Hushpuppi a Dubai saboda Hushpuppi wanda ya fito a matsayin dan kasuwan gidaje kuma da samfurin Model don ba da shawara ga masu zanen kaya da jakunkuna, wanda ke dimbin mabiya masu bibiyar Social Media. Kowa ya gani an gabatar da fitattun ‘yan Najeriya da ke ziyartar Dubai. Hotunan sa tare da wadancan fitattun ‘yan Najeriya a duk fadin intanet yayi yawo Amma sai Abba Kyari ake magana.

Dan Allah ‘yan Najeriya ku yi watsi da duk wadannan labaran karya da ake daukar nauyinsu daga kafafen sada zumunta da ke fitowa daga “Madogarar boye ta Cikin-ciki da ba’a gani kuma a jira sanarwar hukuma daga hukumar ‘yan sanda ko kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya.

ALLAH Ya Albarkaci Nigeria.

Rubutawa Barr JOSEPH B Donald
fasara Mikiya

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: