Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA ƊUMI-ƊUMI: Abdul'aziz Ganduje Ya Kai Ziyara Bangaren Su Shekarau Wato G7

DA ƊUMI-ƊUMI: Abdul’aziz Ganduje Ya Kai Ziyara Bangaren Su Shekarau Wato G7

Daga Comr Nura Siniya

Babban Ɗan gwamnan kano, Abdul’aziz Abdullahi Umar Ganduje, ya koma bangaren tafiyar tsohon gwamnan kano Mal. Ibrahim Shekarau da akewa laƙabi da G7 tare nuna rashin gamsuwarshi akan yadda ake tafiyar da al’amurran gwamnatin a jihar.

Tuni dai Abdul’aziz Ganduje ya kai ziyarar mubaya’a ga Sanatan mazaɓar kano ta Arewa Sen. Bara’u Jibril Maliya a gidan shi da ke jihar kano.

Idan baku manta ba a ƙwanakin baya dai Abdul’aziz Ganduje ya kai ƙarar mahaifiyarsa Prof. Hafsat Ganduje inda ya aikewa da hukumar yaƙi da masu yi ma tattalin arziƙin kasa ta’annati EFCC wasiƙa domin bincikarta akan zargin badaƙalar waɗansu filaye da kuɗaɗe.

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: