Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA ƊUMI-ƊUMI: Abdulmalik Tanko ya musanta garkuwa da kuma kashe Hanifa

DA ƊUMI-ƊUMI: Abdulmalik Tanko ya musanta garkuwa da kuma kashe Hanifa

Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe dalibarsa, Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, ya musanta garkuwa da kuma kashe ta.

A yau Litinin ne a ka sake kawo Tanko, da abokan aikata laifin da a ke zargi, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin Alƙali Usman Na-Abba.

Bayan da a ka karanto musu tuhume -tuhumen da a ke yi musu, dukkan su sun musanta.

Da a ke tuhumar Tanko cewa ya yi garkuwa da kuma kashe Hanifa, sai ya ce “ban aikata ba.”

- Advertisement -

Ƙarin bayani na nan tafe…

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: