Daga Muryoyi
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA na neman babban Jami’in dan sandan Najeriya DCP Abba Kyari ruwa a jallo
Kodayake dai babu cikakken bayani amma Kakakin shugaban hukumar NDLEA ta kasa Mahmud Isa Yola ne ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa “Hukumar NDLEA tana neman DCP Abba Kyari ruwa a jallo”
Lamarin ya yamutsa hazo inda jama’a ke ta neman karin bayani sai dai duk yunkurin da Muryoyi tayi domin jin karin bayani abun ya faskara
- Advertisement -
Binciken Muryoyi ya gano ana zargin DCP Abba ne da laifuka da suka shafi miyagun kwayoyi