Daga Muryoyi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta umurci duka jam’iyyun siyasar kasarnan su gabatar mata da sunayen yan takararsu na Shugaban kasa da Gwamnoni kafin nan da 18 ga watan Yunin shekarar nan
Muryoyi ta ruwaito hukumar zata kammala karbar sunayen wadanda zasu yi takarar shugabancin kasa na duka jam’iyyu a 2023 a watan Yuni kamar yadda doka ta tsara domin kammala shirye shirye.
A yanzu dai kenan kowace jam’iyya da take son tsaida dan takara tana da ragowar watanni 4 su kammala zaben fidda Gwani wanda zai yi takarar shugabancin Najeriya a babban zaben 2023
- Advertisement -