Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Kungiyar ASUU ta rufe duka jami'o'in Najeriya ta tsunduma yajin...

DA DUMI-DUMI: Kungiyar ASUU ta rufe duka jami’o’in Najeriya ta tsunduma yajin aikin wata Daya

Daga Muryoyi

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya wato Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta shiga yajin aiki na tsawon wata guda a matsayin gargaɗi ga gwamnatin tarayya.

Muryoyi ta ruwaito Shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Victor Osodeke ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Litinin bayan wata ganawa ta kwanaki Biyu da majalisar zartarwar ƙungiyar ta yi a Lagos.

Malaman jami’ar da suka dakatar da aiki tsawon wata tara a 2020, sun sha kokawa kan halin da ilimi ke ciki a Najeriya, ciki har da maganar albashinsu.

- Advertisement -

Rahotanni sun ce majalisar zartarwa ta ASUU ta fara taron ganawa tun a daren Asabar a Jami’ar Legas (UNILAG), wanda a wurin ne aka cimma matsaya kan matakin da ƙungiyar ta ɗauka.

Tun a farkon watan nan na Fabarairu ƙungiyar ta nemi dukkan jami’o’in ƙasar su ware rana ɗaya domin wayar da kan ɗalibansu game da rashin cika alƙawari da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi musu.

Ta ce har yanzu gwamnatin ba ta cika alƙawuran da yarjejeniyarsu ta ƙunsa ba da suka ƙulla a 2020, ciki har da maganar tsarin biyan albashi da kuma kuɗaɗen gyaran jami’o’in gwamnati a faɗin Najeriya.

Kazalika, malaman na bin gwamnati albashinsu na watannin da suka shafe suna yajin aiki tsakanin 2019 zuwa 2020.

Sai dai wannan mataki ya jawo babbar koma baya ga sha’anin ilimi a Najeriya inda Dalibai da iyayen yara ke kokawa

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: