Daga Muryoyi
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin Gwamnan jihar Mahdi Gusau daga mukaminsa.
Muryoyi ta ruwaito yan majalisa 20 daga cikin su 21 ne suka kada kuri’ar tsige shi a zaman majalisar na yau Laraba
Tsige shi na zuwa ne kasa da awoyi 3 da kwamitin bincike da Babbar alkaliyar jihar Zamfara ta kafa domin su binciki Mahadi game da wasu zarge-zarge da ake yi masa da ya jibanci sama da fadi da dukiyar jihar
- Advertisement -
A dazu kwamitin ya gabatar da rahotonsa wanda Mahadi yaki amsa gayyatar halartar gaban kwamitin domin kare kansa yana mai zargin cewa batun yana gaban kotu
Mahadi ya sha zargin cewa ana yi masa bita da kulli a tsige shi ne saboda kawai yaki komawa jam’iyyar APC