Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Matawalle ya nada Sanata Hassan Gusau sabon mataimakin Gwamnan Zamfara

DA DUMI-DUMI: Matawalle ya nada Sanata Hassan Gusau sabon mataimakin Gwamnan Zamfara

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya nada Sanata Hassan Mohammed Gusau a matsayin sabon mataimakin Gwamnan jihar bayan an tsige Barista Mahdi Aliyu Gusau.

Muryoyi ta ruwaito Sanata Gasau ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a watan Yunin 2021 kuma shine ke wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya a Majalisar dokoki ta tarayya.

A dazu ne dai Majalisar dokokin jihar Zamfara ta sanar da tsige mataimakin Gwamnan jihar bayan yan majalisa 20 daga cikin 24 sun jefa kuri’ar tsige shi.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Kakakin majalisar dokoki ta jihar Zamfara, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce majalisar ta dauki matakin tsige shi ne bayan an same shi da duka laifukan da ake zarginsa dashi.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: