Daga Muryoyi
Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari har gida a daren jiya sun kashe Daraktan ayyuka da gudanarwa na hukumar kula da tsare-tsare da sufuyo da filaye ta jihar Kaduna, Kaduna Geographic Information Service (KADGIS), Malam Dauda.
Muryoyi ta ruwato har karfe 7 na daren jiya Alhamis margayin yana ofis yana aiki ashe na bankwana ne
Rahotanni sun nuna yan bindigar su kimanim Biyar sun kutsa gidan margayin dake Barakallahu a karamar hukumar Igabi suka iske shi har daki suka harbe shi da bindiga ya mutu.
- Advertisement -
Sai dai abunda ya bawa kowa mamaki shine akwai motoci da sauran kadarori a gidan mamacin amma ko tsinke makasan basu dauka ba sannan basu taba maigadin gidan ko iyalinsa ba.
Muryoyi ta ruwaito Hakimin unguwar, Alhaji Muhammad Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.