Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDubban matasan Arewa Maso Gabas sunyi mubaya'a: Takarar Yahaya Bello don matasa...

Dubban matasan Arewa Maso Gabas sunyi mubaya’a: Takarar Yahaya Bello don matasa ce -inji Asuku

Shugaban Ma’aikata Gwamnan jihar Kogi, Pharm. Jamiu Asuku ya yi kira ga Matasan Najeriya dasu goyi bayan Gwamna Yahaya Bello domin zama Shugaban kasa a zaben 2023.

Asuku ya bayyana hakan ranar Asabar a Gombe a lokacin da Ƙungiyar dake rajin ceto Najeriya reshen yankin Arewa maso Gabas wato-North East Chapter of Rescue Nigeria Mission (RENMISS), ƙungiyar matasa dake goyon bayan kyakkyawan shugaban ci na Matasa ta kawo wa Gwamna Yahaya Bello na Jahar Kogi ziyara, domin ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.

Asuku yace matasa dole su fara dubawa tare da goyon bayan ɗan uwansu matashi domin samun matsayi a siyasa a Babban Zaɓe mai zuwa.

Shugaban Ma’aikatan yace akwai buƙatar matasa dasu yi gangami su faɗakar tare da wayar da kai, akan ƙudirin tsayawa takarar Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello, yana mai cewa shine kadai da zai sanya kasar nan a turbar data dace.

- Advertisement -

Yace “Gwamna Yahaya Bello shi kaɗai ne wanda zai bayar da shugabanci na gari idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa a Babban Zaɓen Shekarar 2023.”

Yace babu wani wuri duk fadin Kasar nan, kamar yadda ake ta Son matasa su yi Shugabanci “Gwamna Yahaya Bello ya baiwa Mata da Matasa damar su zama Shuwagabanni, zai yi Shugabanci nagari idan aka zaɓe shi a Babban ofishi irin Shugaban Ƙasa.

Shugaban Ma’aikatan duk da shi ya wakilci Gwamna, yace Yahaya Bello mutum ne da Shuwagabancin sa na Najeriya zai amfani matasa matuka sosai.

Yace ƙudirin Gwamnan na Matasa ne wanda suke a shirye domin cigaban Ƙasar

“Ina matuƙar godiya da ƙoƙarin Ƙungiyoyin Matasa da dama na tsayawa domin samar da Najeriya ingantacciya a shekarar 2023. A wannan mataki, dole muce akwai buƙatar samun Ɗan takara matashi wanda ke da ƙwazon mulkar ƙasar nan daga matsalolin data ke fama dashi a halin yanzu — Gwamna Yahaya Bello shine mutumen da yayi dai-dai da hakan.”

Ya jaddada cewa Gwamnan ya kuma karya lagon rikicin ƙabilanci a Jahar, Kuma ya nuna cewa shi cikakken ɗan Najeriya ne mai adalci wajen bada muƙaman sa, daya ƙunshi Ƙabilai da dama, da kuma ƙoƙarin sa na magance matsalar tsaro.
Babban Jami’in Ƙungiyar A. S. Dambat wanda ya jagoranci sauran Shuwagabannin Ƙungiyoyi na Yankin Arewa maso Gabas ya yabawa Gwamnan da irin namijin ƙoƙarin sa wajen cigaban garuruwa, Tsaro, da ilmi, da kuma inganta rayuwar Matasa da Mata da sauran abubuwa da dama.
Sun goyi bayan Gwamna Yahaya Bello a matsayin ɗan takarar su, da kuma keda jajircewa ta gogewa ba jagorantar Najeriya, tare da fito da’ita daga matsalolin da take fuskanta a Ƙasar.

Mai baiwa Gwamnan Jahar Kogi Shawara akan Matasa da Harkokin Ɗalibai Kwamared Ahmadu Jibril wanda ya yi jawabin bude taro, ya bayyana irin nasarorin da Gwamnan ya samu da gina gari, da lafiya, da Matasa, da Mata, da bada tallafi, da ilmi, da tsaro, da kuma yanda ya tunkari Cutar Covid-19 wanda ta kawo tsaiko a tattalin arzikin Duniya.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: