Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEFCC ta Karbe Kadarorin Naira Miliyan 104 daga wani Ma'aikacin Gwamnati

EFCC ta Karbe Kadarorin Naira Miliyan 104 daga wani Ma’aikacin Gwamnati

Daga Muryoyi

Wata kotu a Abuja ta baiwa hukumar EFCC umarnin karbe wasu kadarori na filaye biyu da kudinsu ya kai Naira Miliyan Dari da Hudu na wani ma’aikacin hukumar tattara kudaden haraji, FIRS, Aminu Side Garunbabba.

Wadanda ake tuhuma sun karbi kudi har miliyan dari uku da arba’in da daya daga hukumar FIRS a matsayin kudin tafiye tafiyen da bai yi su ba inda suka karkatar da kudin don biyan bukatun su da siyan kadarori.

Da yake yanke hukunci akan batun Mai shari’a Obiora Egwuatu na babbar kotun tarayya dake Abuja ya bayar da umarnin inda ya yanke hukuncin cewa bukatar da lauyan hukumar EFCC ya gabatar Ekele Iheanacho ta yi daidai da sashe na 17 na dokar hana zamba ta 2006.

- Advertisement -

Kotun Ta bayar da umarnin buga kadarar da aka kwace na wacin gadi a wasu jaridun kasar da nufin cewa duk mai kadarar ya fito fili ya bayyanawa kotu dalilin da yasa ba za’a karbe kadarar a mikawa gwamnatin tarayya ba.

Mai shari’ar ya daga karar zuwa 23 ga watan Maris, 2022, don sauraren bukatar karbe kadarorin a mikawa gwamnatin na dindindin.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: