Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEl-Rufai ya ce kan APC a haɗe yake wajen ganin 'Peoples Destruction...

El-Rufai ya ce kan APC a haɗe yake wajen ganin ‘Peoples Destruction Party’ ba ta dawo kan mulki ba

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce gwamnonin APC sun amince da sabon ranar da aka sanya domin ganatar da babban zaben jam’iyyar APC wato 26 ga watan Maris mai zuwa.

Gwamnan ya kuma ce jam’iyyar APC ta amince ta rarraba muƙaman da babu kowa a kai a Kwamatin Ƙoli na jam’iyyar tsakanin Kudu da Arewa kafin babban taronta na ƙasa.

Da yake jawabi ga manema labarai Jim kadan da Gwamnonin suka yi wani taro na musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari yau Talata a fadarsa,

- Advertisement -

El-Rufai ya ce “Bayan ganawarmu da shugaban ƙasa a yau (Talata), mun haɗu a kan abu ɗaya. Mun amince da wani tsari mai adalci da kuma ingantacciyar hanyar rarraba muƙamai ga dukkan sashen siyasa,”.

“Mun amince da wani tsari na karkasa muƙamai ga dukkan shiyyoyin siyasa. Shiyyoyin Arewa za su samu muƙaman da na Kudu suka riƙe a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma (na Kudu) haka,” a cewar Gwamna El-Rufai.

“Cikin ikon Allah nan da 26 ga watan Maris za mu gudanar da babban taro na ƙasa.

“Babu wata tantama cewa kan gwamnonin APC a haɗe yake wajen yunƙurinmu na tabbatar da cewa ‘Peoples Destruction Party’ ba ta dawo kan mulki ba.”

Gwamna El-Rufai ya ce ba zai yiwu a tara gwamnoni har 22 ba “kuma a ce ba a samu bambancin ra’ayi ba”.

“An samu bambancin ra’ayi tsakanin gwamnonin APC game da lokacin taron,” in ji El-Rufai kamar yadda mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan kafafen sada zumunta Tolu Ogunlesi ya ruwaito shi yana faɗa.

Ya ƙara da cewa: “Wannan kuma wai shi ‘yan jarida ke kira gwamnoni marasa haɗin kai. Babu yadda za a yi a tara gwamnoni 22 kuma kowa ya amince da kowane irin ƙudiri. Za a iya samun bambanci amma idan aka kira shi rabuwar kai to an wuce gona da iri.”

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: