Daga Muryoyi
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya haramtawa hukumar kula da ababen hawa KASTLEA rike sanda ko gora ko wani makami a lokacin aikinsu,
Kazalika an umurcesu da su cire duk wasu shingayen bincike da suka saka a hanyoyi sannan daga yanzu an haramta masu sanya kowane nau’in shingen binciken ababen hawa a duk titunan fadin jihar Kaduna
Muryoyi ta ruwaito shugaban sashin ayyuka CMA A.A Manga ya aike da takardar umurni ga kowane Kwamnadan rundunar akan wannan umurni
- Advertisement -
A karshe sanarwar ta kara jaddada wa jami’an KASTLEA cewa an haramta masu binciken ababen hawa daga karfe 8 zuwa 10 na safiyar kowace rana domin saukakawa ma’aikata da dalibai isa wajajen ayyuka da makarantunsu akan lokaci