Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEl-Rufai yace matsalar tsaro na hana shi barci ya fadi matakin da...

El-Rufai yace matsalar tsaro na hana shi barci ya fadi matakin da zai dauka

Daga Muryoyi

El-Rufai ya roki Buhari ya kafa “theatre command” a shiyyar Arewa don kawo karshen ta’addancin yan bindiga

Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nemi Gwamnatin tarayya ta taimaka wa jami’an tsaro da kayan aiki, sannan a kafa wata runduna ta musamman wato “theatre command” kamar yadda ake da ita a Maiduguri don ta riƙa kula da jihohin Arewa Maso Yamma.

Gwamnan a wata hira da manema labarai ya ce idan aka lura matsala ɗaya ake fama da ita a wadannan jihohin da kuma Jihar Naija kuma wannan matsalar garkuwa da mutane kullum ƙaruwa yake yi.

- Advertisement -

Gwamna El-Rufai a don haka ya roki a kara yawan sojoji da yan sanda domin wadanda ake dasu basu isa ba.

Sannan ya yaba wa jami’an tsaro bisa namijin kokari da suke yi ya kuma roki a kara masu kayan aiki, A cewarsa “mu a matakin jiha muna iya bakin kokarinmu wajen basu abinda suke bukata iya karfinmu”

Muryoyi ta ruwaito El-Rufai ya ce ta’addancin da ake yi a Arewa maso yamma na kashe mutane da hana su zuwa gonaki a yanzu ya fi damun jama’a fiye da boko Haram

Ya kuma baiwa jama’a hakuri bisa tsauraran matakan da Gwamnati ke dauka musamman toshe layukan sadarwa, rufe kasuwannin mako, sayar da man fetur a jarka da kuma hawa babur, yin hakan ne ya zama wajibi domin tsare dukiya da rayuka jama’a.

Gwamna Nasir El-Rufai ya roki jama’a su taimaka wajen dakile masu baiwa yan ta’adda bayanai (informant) ya ce “Duk wanda aka ga baya aikin fari amma yana kashe kudi a fada mana (hukuma) zata bincike shi kuma a dauki matakin da ya dace

“Wallahi kullum muna bacci kuma muna tashi da wadannan matsaloli na tsaro domin mu ga karshensu, Allah ya kawo mana karshensu” inji Gwamnan

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: