Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuGanduje kadangaren bakin tulu ne a APCn Kano

Ganduje kadangaren bakin tulu ne a APCn Kano

Ra’ayin: Yasir Ramadan Gwale

Wato a irin yadda Ganduje ya dinga yin kalamansa babu tausasawa ga ‘yan G7 ko “banza bakwai” kamar yadda ya kira su kasan cewar sun wahalar da shi, kuma sun kada masa hantar cikinsa dangane da wannan dambarwa. Shi yasa duk cikin jawabansa babu inda ya nuna zai yi sulhi ko ya nemi su zo a tafi tare domin a gudu tare. Shi yasa duk maganganun da yayi musu suka bayyana irin girman bacin rai da damuwar da yake da ita dangane da wannan dambarwa da ake yi.

Moddibo Ganduje ba kanwar lasa bane, kar yake kallon kowa, kuma mutum ne da ya iya guma cuta. Shi yasa duk wadannan mutanen da suka fafata da shi a batun shugaancin jamiyyar nan sai ya kaisu kasa matukar suka cigaba da kasancewa cikin jamiyyar APC.

Mafitar G7 daya ce, su fice daga cikin jamiyyar APC su koma PDP domin nan ne kadai zasu iya rama abinda Ganduje yayi musu, amma idan ba haka ba Moddibo Ganduje sai ya gama da su daya bayan daya, kun dai ji abinda ya fada da bakinsa cewar “Tsiyar Nasara” to wannan nasaran irin tsiyar da zai musu matukar suka cigaba da kasancewa cikin jamiyyar da yake matsayin jagoranta to, shakka babu, ba kadan bace.

- Advertisement -

Dangane da batu wannan Shari’a, mutane da dama suna ganin kamar bangaren G7 ne zasu yi nasara a wannan dambarwa ta jamiyyar da ake fama da ita a jihar Kano. Saboda watakila a karon farko anga alamun nasara a tattere da su, Amma magana ta gaskiya daman da wuya ace uwar jam’iyyar APC ta kasa ba zata taba yin kasassabar wofantar da Gwamna ta kama ‘yan majalisu ba.

Domin Moddibo Ganduje a matsayinsa na Gwamna, illar da zai iya yiwa Jam’iyyar APC babu wani cikin masu hamayya da shi a G7 da zai yi mata irin illar da zai yi mata idan ta wofantar da shi ta kama bangaren G7. Domin halin da ake ciki a cikin Jam’iyyar APC. Gwamnonin Jam’iyyar dake hannun Gwamna Mai Mala Buni, suna son dora dan takarar shugaban kasa daga bangaren su, wanda a cikin wannan aniya tasu dole suna bukatar hadin kan dukkan abokansu Gwamnoni na APC.

A matsayin jihar Kano na babbar jihar da take bayar da kuri’a sama da kowace jiha a Arewa, ba zasu taba yadda suyi sakaci ta kubuce musu ba ta hanyar wofantar da Gwamnan ta mai ci, su kama ‘yan majalisu ba. Tun farko, abinda su Mai Mala suke yi a tunani na bai wuce lallaba bangaren Malam Shekarau ba, dan kar su kubuce saboda ba wanda yake son yayi asarar mutum ko ya yake a wannan yanayin da 2023 ke kara kusantowa. Amma ba wai dan sun san su ne da nasara ba.

A halin da APC take ciki, Gwamna Ganduje ya zama kadangaren bakin tulu a cikin Jam’iyyar, idan an karshi to an kar jamiyyar a Kano, idan an barshi to tilas a hakura da zabin da ya yiwa kansa na (watakila bin ra’ayi sabanin na sauran Gwamnonin Jam’iyyar) wanda hakan ne zai kai APC ga asara a jihar Kano musamman idan G7 sun sauya sheka zuwa PDP.

Domin da APC ta hana Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha Jam’iyyar a hannun sa, aka hana shi saka dan takarar da yake so, karshe ya yiwa jamiyyar wawar asara in banda daga bisani sun samu hukuncin kotun koli, irin haka ce ta faru a jihar Oyo nan ma Jam’iyyar tayi wawar asara a sakamakon rikicin da ake da Gwamnan jihar.

Don haka, dole APC su yi taka tsantsan da Ganduje domin nasara ne, tsiyarsa yawa gare ta. Amma tare da goyon bayan G7 idan suka sauya sheka zuwa PDP kuma APC ta tsayar da dan takarar shugaban kasa wanda basa d’asawa da Ganduje, abu ne mai sauki ya taimaka a kayar da APC a Kano a zaben shugaban kasa.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: