Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuGASKIYAR MAGANA: Musulmi ya kamata hankalinmu ya dawo jikinmu!!!

GASKIYAR MAGANA: Musulmi ya kamata hankalinmu ya dawo jikinmu!!!

GASKIYAR MAGANA!!!

Daga Dalhatu Kasimu Imam

Limamin masallacin Zariya.

 

Da fatan mun wayi gari lafiya a wacannan rana mai albarka, Jumu’ah babbar rana.

- Advertisement -

Muna roƙon ALLAH Maɗaukakin Sarki da Ya yaye mana dukkan abubuwan da suke damunmu a wacannan ƙasa tamu – Nigeria.

Mutun kan tashi ne a mafiyawancin lokuta akan abinda ya ga ana yi a gidansu ko a maƙwantansu ko kuma daga abokan zama.

1) In mutun ya wayi gari yaga gidansu ana Ɗariƙun Sufaye, zai tashi dashi.

2) In ya wayi gari yaga ana Izalah, dashi zai tashi.

3) In ya wayi gari yaga ana Shi’ah, dashi zai tashi.

4) Duk abinda ya wayi gari ya gani haka zai ɗora rayuwanshi a kai………!

Saboda haka, in muka koma ma asalin abinda ya haɗamu na “Musulunci”, mukayi riƙo dashi yadda ya dace, kowwa ya riƙe abinda ya gane, sai mu zauna lafiya. Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) ya ambacemu da “Musulmi” kawai! Bai ambacemu da wasu sunaye ko ƙungiyoyi daban ba.

A ƙabari tambayoyi 3 ne kacal:
a) Ubangijinka
b) Addininka
c) Annabinka

Ba tambaya ta 4 ko fiye!

Baya ga aikata Farillai, duka wani abu da mutun zai aikata ganin damanshi ne, baiyi laifi ba.

In ka tafi aikin Hajji ko Umrah, ba irin wanda baza ka gani na Musulmi ba; mabiya Ɗariƙun Sufaye ne, ko Wahabiyyawa ne ko ƴan Shi’a ne, ko, ko, ko! Kowanne kuma da Saudi Visa ya shiga Saudia a matsayinshi na “Musulmi” faƙaɗ.

Abin takaici mun wayi gari kullun a ƙasar nan tamu sai ƙara gina Masallatai ake da nufin wariya da raba kawunan Musulmi akan abinda bai kai ya kawo ma a kalla ba. Duka akan dalilan neman mulki ko neman kuɗi ko haddasa fitina da gaba a tsakanin Musulmi ko kuma neman goyon baya daga ƴan siyasa. Za muga Masallatan da muke dasu ba ma iya cikawa ma, balle a ce baza a iya faɗaɗawa ba, lallai sai an nemi ƙari.

A yau irin ƙalubalen da Musulunci ke fuskanta ne a duniya ya kamata mu komo mu haɗa kawunammu, muga yadda za mu magance ƙalubalen.

Kuma waɗannan rabe-rabe mu kammu mun tabbatar ba gaskiya ne ba. Don muna haɗuwa a wajen gado da wajen auratayya. Hakanan kuma muna haɗuwa a wajen harkokin zumuntammu da wasu lokuta wajen ɗiban dukiyan al’umma.

Ya kamata Malamai su maida hankali ne wajen saita al’umma akan karkacewa da al’umma tayi a halin da muka samu kawunanmu a yau na gurɓacewan tarbiyya da rushewan kyakkyawan mu’amallah, maimakon yin Wa’azozi na raba kawunan al’umma akan ƴan saɓani kaɗan.

Da akwai mutumin dazai Musulunta da wataƙila 8am, kafin Azahar kuma ALLAH Ya amshi rayuwanshi. Kaga zai tafi Aljannah ba tare da yayi wani aiki na Musulunci ba.

Ashe ko in hakane, toh abinda ya haɗamu na Musulunci, shine wajibimmu. Duka sauran abubuwa kuma kowwa na da irin tasa fahimtar. Fahimtar baza ta kore mutun daga zama Musulmi ba.

Ya kamata hankulammu su dawo jukunammu, mu koma yimma kawunammu abubuwa da suka dace da girmama ra’ayin junammu da yimma junammu uzuri a bisa kura-kurai da baza mu iya rayuwa ba tare dasu ba.

Magabata sun sami saɓani a tsakaninsu na fahimtar wasu daga Nassosin Ƙur’ani, amma hakan bai sanya sun raba Masallatai ko sunci mutuncin junansu ba.

Har kullun mutumin da bai yarda da kai ba, ai ba yadda kai kuma za ka yadda dashi.

Idan aka tafi Lahira, kowwa fah zai ɗauki nauyin abinda ya aikata ne – mai kyau ko mara kyau.

Hakanan kuma kowane mutun yakan mutu ne akan addinin abokin zamanshi. Saboda haka wajibin kowannemmu ne ya duba irin abokin zaman da zai zauna dashi.

Ma’assalamah

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: