Gwamna Yahaya Bello ya amsa zai tsaya takara domin kai Najeriya tudun tsira a 2023

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ya amsa kiran dumbin jama’a dake ta dafifin yi masa mubaya’a da kiraye-kiraye gareshi ya nemi takarar shugabancin Nigeria a 2023

Gwamnan ya bayyana aniyar takarar tasa ce a wata hira da yayi da kungirar yan jaridan Hausa a yau Juma’a

Bayanin na Gwamnan na zuwa ne a daidai lokacinda Jama’a daidaiku da kungiyoyi daga ko ina a sassan Nigeria ke cigaba da bayyana imaninsu akan cewa shine yafi dacewa ya gaji shugaba Muhammadu Buhari saboda kyawawan halayensa, kwazonsa, kazar-kazar dinsa da kuma iya mulki

- Advertisement -

Kiyasin baya-bayan nan ya nuna Gwamna Yahaya Bello wanda ake yiwa lakani da matashi na matasa farinjinin sa na kara hau-hauwa duk da yarfen siyasa da yake fuskanta

“Ina sanar da ku na amsa kiran ku kuma zanyi takara in sha Allahu a 2023” inji Gwamnan

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: