Daga Muryoyi
Gwamnatin tarayya ta ce kamfanin mai na NNPC ya samu isasshe kuma wadataccen man fetur da zai rarrabawa gidajen mai a faɗin Kasarnan.
NNPC ya buƙaci yan Najeriya sun kwantar da hankalinsu akwai isasshen man fetur kuma kamfanin na aiki da abokan hulɗarsa don tabbatar da cewa ya isa a kowane ɓangare na ƙasar.
Kamfanin ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya su ci gaba da haƙuri yayin da ake ƙoƙarin ganin abubuwa sun koma daidai.
- Advertisement -
An shafe kusan mako biyu ana wahalar man fetur a sassan Najeriya wanda hakan ya jawo kunci da damuwa.