Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuHATTARA DAI JUMA'A: An kama dan sandan bogi dake karbe ababen hawan...

HATTARA DAI JUMA’A: An kama dan sandan bogi dake karbe ababen hawan mutane yana sayar wa a Kaduna

Daga Muryoyi

Rundunar yan sanda a Kaduna sun kama wani mutum dake yin sojan gona da sunan shi dan sanda ne yake kafa shinge yana kama ababen hawa musamman Babura,

Muryoyi ta ruwaito dubun mutumin ta cika ne a jiya Asabar lokacinda ya kama wani mai babur “ba tare da yasan waye shi ba”

Lamarin ya faru ne a Unguwar Malali Kaduna inda aka garzaya da wanda ake zargin zuwa ofishin yan sanda na shiyyar da abun ya faru kafin daga bisani aka tafi dashi hedkiwatar yan sandan jihar,

- Advertisement -

Wani jami’in dan sanda ya kaure da farinciki bayan faruwar abun domin a cewarsa “an dade ana kawo kara a ofishinmu cewa wai ina karbe baburan mutane in gudu da su har bayan kanta an taba jefa ni saboda yadda mutane suka rika kawo kara tun ina iya kare kaina har na ma rasa ne zan ce.”

Jami’in wanda ya kara da cewa shi kanshi da yaga barawon dake sojan gonar ya gane dalili “munyi kama dashi, zai yi wuya ka iya fayyace mu” ashe shi yasa mutane ke cewa nine na karbam masu babur da sun ganni”

Barawon babur din wanda ba Bahaushe bane ya rika kwarmata ihu a sadda aka kama shi inda alamu suka nuna idan ya karbi babur din mutum sai yace masa su hadu a ofishin yan sanda na Malali domin ya karbi abunsa daga nan shi kuma ya gudu da babur din idan ya samu dama ko kuma ya karbi na goro ya saki babur din.

Faruwar wannan lamari ya ja hankulan Jama’a a inda suke ganin ya kamata idan yan sanda zasuyi aikin kame ko jami’an hukumomin hanya irinsu KASTLEA su rika saka akalla kaki ko wata babbar shaida da za a gane cewa ba yan damfara bane ko masu sojan gona irin wannan da aka kama

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: