Za A Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisun Tarayya A Ranar 25 Ga Fabrairu, 2023, Za A Gudanar Da Zaben Gwamnoni Da Na ‘’Yan Majalisun Jihohi A Ranar 11 Ga Maris
Daga Comr Abba Sani Pantami
A yau Asabar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana sabbin ranakun da za a gudanar da zabukan shekarar 2023.
Shugaban INEC na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai yau a Abuja.
- Advertisement -
Ya ce a yanzu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar 25 ga Fabrairu, 2023, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga Maris, 2023.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa sabuwar ranar ita ce a ba da damar yin daidai da tanade-tanaden dokokin zabe da suka kayyade cewa a buga sanarwar zabe akalla kwanaki 260 kafin zaben.
Shugaban na INEC ya kuma ce za a kuma buga ka’idojin zaben nan gaba kadan.