Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuJami'ar Kwara ta kori dalibin ajin karshe da aka kama yana rubutawa...

Jami’ar Kwara ta kori dalibin ajin karshe da aka kama yana rubutawa Budurwarsa jarabawa

Daga Muryoyi

Jami’ar jihar Kwara UNILORIN ta kori wani dalibi dan ajin karshe wato 400 level daga Jami’ar saboda kamashi yana rubutawa budurwarsa jarabawa.

Kodayake an sakaye sunan dalibin da kuma budurwar da yake rubutawa jarabawar amma dai wani da ya shaida faruwar abun ya rubuta a shafinsa na twitter.

Muryoyi ta ruwaito @_MayorBaby ya wallafa labarin a shafinsa na twitter inda ya yi Allah wadai da sokoncin da abokin nasu yayi “soyayya ta ja masa nadama har karshen rayuwarsa”

- Advertisement -

Mayor ya ce dalibin ya rubutawa dalibar jarabawar GNS112 wanda hakan ya jawo masa kora a madadin takardar shaidar kammala karatu

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: