Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKanawa sun yi wa Yahaya Bello mubaya'a 2023 saboda "shine kadai ya...

Kanawa sun yi wa Yahaya Bello mubaya’a 2023 saboda “shine kadai ya damu da damuwar talaka a Najeriya”

Daga Muryoyi

An gudanar da taron dandazon mata da matasa a Kano na magoya bayan Gwamnan Yahaya Bello dake neman ya tsaya takarar shugabacin kasa a 2023 saboda cancantarsa da salon iya mulkinsa

Taron ya gudana ne a yau Asabar a karkashen kungiyar Rescue Nigeria Mission dake yada da’awar takarar Gwamnan a fadin Nigeria

Jagoran kungiyar na jihar Kano Abdul Amat Maikwashewa ya bayyana cewa su ne suka roki Gwamna Yahaya Bello ya fito takara a 2023 bisa la’akari da cancantarsa a kowane fanni, gashi matashi mai jini a jika, ya kware wajen iya shugabanci sannan uwa uba shine shugaban da ya damu da damuwar talaka.

- Advertisement -

Maikwashewa yace Gwamnan ya janyo mata da matasa a jikinsa kuma ya dage wajen ganin ya bunkasa rayuwar matasan Nigeria gashi baya kyamar jama’a sannan ya kirkiri kyawawan kudurori da manufofi na cigaban jama’a.

A cewar jagoran matasa zasu amfana gaya muddin Yahaya Bello ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya ce ko a lokacin zabukan kananan hukumomi a jiharsa ta Kogi ya baiwa mata da matasa dama kuma sun ci zabuka rututu a jihar.

Da yake nasa jawabin a wajen taron Shugaban ma’aikatan Gwamnan Kogi Abdulkarim Jamiu Asuku ya yabawa dandazon Kanawa mata da matasan su bisa fitowa kwansu da kwarkwata domin nuna goyon bayansu ga Yahaya Bello

Asuku ya cigaba da cewa lokaci yayi da matasa zasu karbi jagorancin kasarnan ta hannun Gwamna Yahaya Bello.

Abdulkarim Jamiu Asuku ya kara da cewa 2023 dama ce ga matasa su kafa gwamnati, sannan ya ce Gwamna Yahaya Bello ya cancanta kuma zai samar da Gwamnati da zata samar da ayyukan yi ga matasa da tsaro da dai sauransu

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: