Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKashi 60% na malaman makaranta a Borno basu cancanta ba -Zulum ya...

Kashi 60% na malaman makaranta a Borno basu cancanta ba -Zulum ya fadi matakin da zai dauka akansu

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce zai tsakuro malaman da basu cancanta su koyar da yara a makarantu ba, ya ba su aikin shuka bishiyoyi karkashin ma’aikatar muhalli a jihar.

Hakan na faruwa ne bayan da aka fitar da wani rahoto wanda ya nuna cewa kashi 31 daga cikin malaman jihar ne kawai suka cancanta su koyar da yara.

Ko a watan Disamba wani kwamitin da Gwamna Zulum ya kafa domin tantance malaman makarantun Gwamnati a fadin jihar Borno ya bayar da rahoton cewa kashi 60 na malan dake koyarwa a makarantun jihar basu cancanta ba.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito a cewar shugabam Kwamitin, Dr Shettima Kulima, daga cikin Malamai 26,250 da aka tantance an gano dubu 10,103 kadai suka tsallake suka cancanta da malumta.

Kulima ya ce mafi yawansu basu da isassun takardun kammala karatu, wasun su kuma sun tsufa kuma sunki yin ritaya, sannan wasun su takardun bogi ne dasu har wayau kuma wasu daga cikin malaman sunyi yara dayawa a yayinda wasunsu kuma ke aiki a fiye da makaranta daya.

Shugaban Kwamitin ya shaidawa Zulum cewa sun bayar da shawarwari guda 30 na matakan da za a iya dauka akan malaman da kuma bangaren ilimi a jihar domin tsaftace shi.

A cewar Kulima bayan tantancewar kudaden da ake kashewa Malan zai ragu daga Naira miliyan N693.1m zuwa Naira miliyan N427.8m.

Sai dai daga bisani an ruwaito Gwamna Zulum na cewa “Ba zai Kori Malamam makarantar da basu cancanta su koyar din ba a makarantu, Mai makon haka zai debesu daga Makarantu zuwa wasu ma’aikatan ba tare da an taba kudaden Albashin kowa ba.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: