Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKungiyar malaman framare, NUT sun gudanar da alkunuti ga Shugaba Buhari Allah...

Kungiyar malaman framare, NUT sun gudanar da alkunuti ga Shugaba Buhari Allah ya tunsar dashi ya cika masu alkawarin karin albashi

Daga Muryoyi

Kungiyar malaman Framare ta kasa, NUT sun gudanar da jerin addu’oi a yau Talata a Abuja domin neman Allah ya taba zuciyar shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawurran da ya dauka na kara masu albashi da kuma kara shekarun ritaya

Majiyar Muryoyi ta ruwaito Gwamnatin Buhari tayi wa malamai alkawari a jawabinsa na ranar malamai ta duniya a 2020 da 2021 cewa Gwamnatin tarayya zata gyarawa malamai kudaden albashinsu zuwa mafi karancin albashi dubu 30 (N30,000)

Sannan kuma Buhari ya yi allawari zai inganta kudaden alawus-alawus din malaman framare da sauran batutuwan da ya shafi malaman.

- Advertisement -

Gwamnatin tarayya a watan Disamba bara 2021 ta ce daga watan Janairun sabuwar shekara 2022 Shugaba Buhari zai sanya hannu kan gyare-gyaren kudade da shekarun ritayar malaman kuma daga watan 1 zasu fara samun sabon albashin amma sai gashi har yanzu shiru.

Kungiyar NUT ta shirya taron addu’oi da alkunutin ne a Abuja inda Sheikh Khalid Aliyu da Adebayo Osijo suka jagoranta.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: