Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKuri'u milyan 25 daga yanki Kudu maso Gabas na Yahaya Bello ne...

Kuri’u milyan 25 daga yanki Kudu maso Gabas na Yahaya Bello ne –inji Kungiyar matan Igbo

Daga Muryoyi

Kungiyar matan kabilar Igbo sun sha alwashin baiwa Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kuri’u miliyan 25 daga yankinsu na Kudu maso Gabas muddin ya tsaya takarar shugabacin kasa a 2023.

Shugabar kungiyar “Igbo Women Forum” Lady Uju Obi a ranar Lahadi ta ce sun shirya wata gagarumar zanga-zangar nuna goyon baya ga takarar Gwamnan a Abuja kwanan nan.

Lady Uju ta cigaba da cewa cikin manyan dalilan da yasa suke son Yahaya Bello shine son zaman lafiya da hadin kan kasa da kuma yadda ya damu da matsalar tsaro

- Advertisement -

A cewar ta a jiharsa ta Kogi ya dakile duk wata matsala ta tsaro kama daga harin yan bindiga, satar mutane da garkuwa dasu da sauransu.

Sannan shine dan siyasar da ke da farin jini a duka kasarnan gashi matashi mai jini a jika, matashi na matasa wanda ya damu da damuwar mata da matasan Najeriya.

Kungiyar ta roki jam’iyyar APC ta dakatar da batun tsarin kai kujerar shugaban kasa yankin Kudu,

Lady Uju ta ce zasu je su samu duk yan takara da deliget na yankin Inyamurai su marawa Yahaya Bello baya a 2023 domin dorewar dimokuradiyya

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: