Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMajalisar dokokin Zamfara ta aikawa mataimakin Gwamnan jihar takardar tsige shi

Majalisar dokokin Zamfara ta aikawa mataimakin Gwamnan jihar takardar tsige shi

Daga Muryoyi

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta aika wa mataimakin Gwamnan jihar Mahadi Gusau sanarwar soma shirin tsige shi daga mukaminsa,

Kakakin majalisar, Shamsudeen Hassan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Ya ce majalisar ta dauki matakin tsige mataimakin Gwamnan ne sakamakon zarginsa da rashin biyayya, da badakalar kudade da kuma cin amanar ofis da ya saba dokiki tsarin mulkin Nigeria sashi na 190 da na 193 (1), (2) (a)(b)(c).

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Zamfara, Musa Bawa ne ya gabatar da kudirin dokar neman a tsige mataimakin Gwamnan a ranar Juma’a da ta gabata inda Kakakin majalisar ya sha alwashin zartar da hakan amma a bisa tsarin dokar kasa.

To sai dai Muryoyi ta ruwaito wani hadimin mataimakin Gwamna, Umar Aminu, ya shaidawa manema labarai cewa “basu karbi wata takardar sanarwar tsigewa daga majalisar dokokin jihar ba”

Ya ce suna ofis a jiya Litinin tare da mataimakin Gwamnan amma babu wanda ya sanar da su. Yace ko a jiya sai da lauyan Mataimakin Gwamnan ya tunashe da majalisar umurnin da kotu ta bayar cewa “kada su tsige mataimakin Gwamnan”

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: