Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMatashi A Gombe, Ya Shake Mahaifiyarsa Ta Mutu Saboda Ta Yi Masa...

Matashi A Gombe, Ya Shake Mahaifiyarsa Ta Mutu Saboda Ta Yi Masa Fada  Ya Daina Shaye-shaye

Daga Comr Abba Sani Pantami

A jiya Laraba, hukumar ‘yan sanda reshen jihar Gombe ta jera wasu mutum takwas da ta kama da laifi daban-daban a faɗin jihar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ɗaya daga cikinsu, Garba Abubakar, ya shiga hannu ne bisa zargin shakare mahaifiyarsa, Salamatu Abubakar, yar shekara 45.

Kwamishinan yan sandan jihar Gombe, Ishola Babaita, ya ce wanda ake zargin ya yi wa mahaifiyarsa haka ne saboda ta masa faɗa ya daina shan miyagun kwayoyi.

- Advertisement -

“Wanda ake zargi ya shake mahaifiyarsa ne saboda ta masa faɗa ya dena ta’amali da miyagun kwayoyi. An yi gaggawar kai matar babban Asibitin Kumo, amma likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa.”

“Ina shawartar iyaye su maida hankali da sa ido wajen kula da ‘ya’yan su kuma su tabbatar ba su faɗa muguwar ɗabi’ar shan miyagun kwayoyi ba.”

“Babban abun takaici wannan matar ta rasa rayuwarta a hannun ɗan da ta tsugunna ta haifa, ɗaya ne daga cikin sharrin kwayoyi.”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: