Muna Ƙira Ga Gwamnatin Najeriya Da Ta Gaggauta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Malaman Jami’o’i ASUU

Muna Ƙira Ga Gwamnatin Najeriya Da Ta Gaggauta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Malaman Jami’o’i (ASUU)

…Babu yadda za’a yi ‘yayan talakawa su samu ingantacciyar rayuwa matuƙar suna zaune a gida kara zube, ba tare da sunyi karatu ba.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar marubutan Arewa “Arewa Media Writers” ƙarkashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, ta na ƙira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kawo ƙarshen yajin aiki na gargadi da malaman jami’o’i suka shiga na tsawon kwanaki 30 (ASUU) wanda suka tabbatar da cewa matuƙar Gwamnatin ƙasar bata biya su hakkokinsu ba zasu shiga yajin aikin sai Baba ya gani.

- Advertisement -

Me yasa malaman jami’o’in suka shiga yajin aiki?

Taƙaitaccen bayani daga H. M. Khalid Malami a jami’ar Abubakar Tabawa Balewa dake jihar Bauchi

 

Malam jami’o’i sun zargi gwamnatin ƙasar da gaza bawa jami’o’i muhimmancin da ya dace don ganin an inganta jami’o’in ƙasar.

Sun zargi Gwamnatin da kasa cika alƙawarin yarjejeniyar da suka yi da ita, tun a shekarar 2009, da wasu alƙawurori a shekarar 2019 da 2020, sannan gwamnatin ta kasa sakin kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’in da tayi alƙawari.

Gwamnatin ƙasar taƙi karɓar tsarin UTAS na malaman jami’o’in domin a saka su cikinshi a madadin tsarin da gwamnatin ta kawo na IPPIS, haka zalika gwamnatin ta kasa biyan alawus din wasu malamai tun daga shekarar 2013 zuwa yau.

Gwamnatin ta kasa magance matsaloli da yawa tun daga kan jami’o’in Tarayya har zuwa na Jihohi.

Wannan shine wasu daga cikin dalilan da yasa malaman jami’o’i suka shiga yajin aikin gagargadi har na tsawon kwana 30 a fadin ƙasar.

Da wannan dalilin ne Ƙungiyar marubutan Arewa “Arewa Media Writers” take ƙira ga gwamnatin ƙasar da ta tausayawa ‘yayan talakawan dake karatu a cikin ƙasar don ganin ta kawo ƙarshen yajin aikin malaman, ta yadda ‘yayan talakawa zasu koma makarantu su cigaba da karatun su, matukar ana son su samu ingantacciyar rayuwa mai inganci.

Idan ‘yayan talakawa basuyi karatu ba, babu yadda za’ayi su samu ingantacciyar rayuwa mai kyau, sai dai su fandare su koma shaye shaye su zama ‘yan ta’adda a cikin al’umma.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: