Naziru Sarkin Waka ya baiwa Ladi Cima kyautar Naira Miliyan Biyu, Fati Slow miliyan daya

Daga Muryoyi

Fitaccen mawaki Naziru Sarkin Waka ya baiwa dattijuwar Jarumar Kannywood Hajiya Ladi Cima kyautar Naira miliyan Biyu N2M domin ta ja jari indai dama tana shiga harakar fim ne domin neman abinci

A cikin wani sabon bidiyo da mawaƙin ya fitar a yau Lahadi Naziru yace “idan har neman abinci ne dalilin da ya sanya Haj. Ladi Cima take fitowa a yin Fim to ni da ƴan’uwana mun yanke shawarar baiwa Hajiya Ladi Cima tallafi Naira Miliyan Biyu domin taje ta ja jari”

Sannan Naziru ya kuma ƙara da cewa itama Jaruma Fati Slow wadda tayi maganganu akansa ya lura tana bukatar taiko don haka “A kafa kwamiti ya zo ya karɓar mata Naira Miliyan 1 domin ita ma ta je taja jari ta kama sana’a”

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Mawakin ya baiwa yan fim hakuri wadanda suka fusata akan maganganun da ya fada a bidiyon da yayi makon da ya gabta inda yace “gaskiya ce kawai ya fada kuma ko gobe ta kama ya fada sai ya fadi” amma kuma a cewar Naziru bai kama sunan kowa ba a batun da yayi cewa wasu yan matan ma sai anyi zina dasu kafin ake saka su a fim

Kawo yanzu dai bayan ruwan martani da Naziru yasha akan wannan maganganu nashi ana kuma rade-radin yan fim din zasu maka shi a kotu domin fayyace zargin da yayi masu da kazafi wanda suka ce hakan na iya jawo babbar koma baya ga masana’antar Kannywood

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: