Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuNIRSAL: Gwamnatin tarayya tayi kira Jama'a su fara biyan kudin tallafin korona...

NIRSAL: Gwamnatin tarayya tayi kira Jama’a su fara biyan kudin tallafin korona da ta basu rance

Daga Muryoyi

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga daukacin yan Najeriya da kamfanoni da suka karbi rancen kudin Korona daga bankin CBN ta hannun “NIRSAL Microfinance Bank” da su hanzarta biyan basussukan kamar yadda suka alkawurranta.

Dama dai a watan Maris din 2020 lokacin Korona babban bankin Najeriya ta hannun NIRSAL ya bayar da rancen kudade ga jama’a da yan kasuwa a karkashin shirin “Targeted Credit Facility (TCF) COVID-19 loans” wanda aka baiwa jama’a domin su farfado daga radadin annobar Korona

Muryoyi ta ruwaito Bankin NIRSAL a ranar Litinin ya fitar da sanarwa cewa “Munyi namu halaccin lokaci yayi da duk wanda ya karbi rance a wajen mu zaku nuna mana halacci ta hanyar maido da kudaden da muka baku rance”

- Advertisement -

Bankin NIRSAL ya rarraba rancen akalla Naira Biliyan N50 billion kudaden rancen tallafin Korona da sharadin wadanda aka baiwa zasu maido dashi.

Wadanda suka amfana da bashin sun hada da matsaigatan yan kasuwa, daidaikun mutane da sauransu, Daga watan Maris zuwa Afrelun 2020 an samu akalla mutum dubu 80 da suka nuna sha’awar neman rancen

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: