Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuObasanjo yace Najeriya na bukatar karin yan tawaye

Obasanjo yace Najeriya na bukatar karin yan tawaye

Daga Muryoyi

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, yace Najeriya na bukatar karin yan tawaye masu tsaurin ido da zasu rika kallon masu mulki suna fada masu gaskiya ba tare da shayi ba,

Obasanjo ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen bikin kaddamar da littafin rayuwar Basaraken gargajiya Babanla Adinni na Egbaland, Chief Tayo Sowunmi mai taken “Footprints Of A Rebel.” wanda ya gudana ranar Asabar a Abeokuta dake jihar Ogun,

Muryoyi ta ruwaito tsohon shugaban kasar na cewa muddin ana so kasarnan ta samu cigaba da kuma habbakar tattalin arziki mai dorewa to akwai bukatar kara samun yan tawaye masu tsaurin ido.

- Advertisement -

Obasanjo ya ce masu rike da madafin iko idanunsu na rufewa a wasu lokutan wanda suna bukatar wanda zai kalle su cikin ido yayi masu bore kan wani abu da suke yi wanda yaga bai dace ba ko kuma zai durkusar da kasar

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: