Rundunar yan sanda ta kama DCP Abba Kyari da tawagarsa ta mika wa hukumar NDLEA

Daga Muryoyi

Hedkiwatar rundunar yan sandan Najeriya ta kama DCP Abba Kyari sannan ta mika shi ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a yammacin yau Litinin

Muryoyi ta ruwaito a safiyar yau ne NDLEA ta ayyana neman DCP Abba Kyari ruwa a jallo bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi hodar iblis da nauyin ta ya kai kilo 25.

Hukumar ta nemi Abba ya kai kanshi gabanta domin fuskantar tuhuma da wasu tambayoyi kan zarginsa da akeyi da hannu a wata kungiyar fataucin miyagun kwayoyi ta kasashen waje.

- Advertisement -

Sauran wadanda rundunar yan sandan ta kama ta mikawa hukumar NDLEA sune DCP Abba Kyari; ACP Sunday J. Ubua; ASP Bawa James; Inspector Simon Agirgba da kuma Inspector John Nuhu

Muryoyi ta ruwaito an kai wadanda ake zargin ne Hedkiwatar hukumar NDLEA da misalin karfe 5 na yammacin yau Litinin domin fadada bincike.

NDLEA ta ce ba zata yi kasa a guiwa ba har sai ta fadada bincike ta bankado tare da kamo duk masu hannu a lamarin ta hukunta su.

A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: