Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSaudiya ta fitar da rukunin waɗanda za suyi aikin hajjin bana 2022

Saudiya ta fitar da rukunin waɗanda za suyi aikin hajjin bana 2022

A yayinda aikin Hajji 2022 ke kara karatowa kasar Saudiyya ta fitar da wasu bayanai a matsayin taba ka lashe kan wadanda take ganin zata bari suyi aikin Hajji da kuma wadanda ba za a barsu suyi aikin Hajjin 2022 din ba

Hukumar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta fitar da rukunin waɗanda ba ƴan Saudiya da ba za su yi aikin Hajjin 2022 ba.

A wata sanarwa da Hukumar ta fitar a jiya, waɗanda su ke da bizar da a ka saba yi idan za a shiga ƙasar, ko kuma mazauna ƙasar da su ke da shaidar iznin zama me kaɗai ne za su yi aikin Hajji.

Hukumar ta ce nan gaba kaɗan za ta sanar da shirye-shirye da tsare-tsare na aikin Hajjin bana ta sahihan kafafen ta na sadarwa.

- Advertisement -

A tuna cewa a bara, mahajjata 60,000, kuma mazauna Saudiya ne su ka yi aikin Hajji, kuma sai da a ka yi wa kowa allurar rigakafin korona karo biyu-biyu.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: