Shugaba Buhari ya cimma matsaya da Yahaya Bello kan batutuwan tsaro da siyasa

Gwamna Yahaya bello ya yabawa Shugaba Buhari kan kokarinsa na dakile ta’addanci a Arewa maso yammacin Nageriya.

A yau ranar Talata ne gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kai wa shugaban kasa Muhammad Buhari ziyara a fadar Aso villa dake Abuja.

A cewar babban sakataren yada labaran gwamnan, Onogwu Mohammed, Bello da shugaba Buhari sun tattauna dalla-dalla kan harkokin siyasa ne dana tsaro.

“Gwamnan, kamar yadda ya saba game da harkokin mulki da tsaro, ya kasance a fadar Villa domin ci gaba da tattaunawa da shugaban kasar Sun yi musayar ra’ayoyi kuma sun cimma wasu matsaya da ba zan bayyana ba don dalilai na sirri inji shi.

- Advertisement -

Wakilin Gwamnan ya bayyana cewa Bello ya yaba da kokarin da Shugaban kasa ke yi na dakile matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma, inda ya kara da cewa nan ba da dadewa ba al’ummar yankin za su fara cin gajiyar wannan kokarin.

Mohammed ya kuma lura da cewa shugaba Buhari cikin Yanayin farin ciki da natsuwa ya tarbi gwamnan.

Yahaya Bello na daya daga cikin masu neman ganin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 kuma ya samu goyon baya daga kungiyoyi daban-daban a fadin kasar nan.

A farkon watan Janairu ne kungiyoyin mata akalla 600 da aka zabo daga sassa daban-daban na kasar suka hallara a Abuja domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Yahaya Bello domin tsayawa takarar shugaban kasar nageriya.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: