Shugaba Buhari zai tafi kasar Turai a yau Talata

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata zai tafi Belgium domin halartar taron haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar haɗin kan Afirka wato African Union (AU) da takwararta wato Tarayyar Turai (EU).

Ana sa ran taron zai gudana a birnin Brussels daga ranar 17 zuwa 18 ga watan Fabarairu da muke ciki,

Kuma ana sa rai shugabannin nahiyoyin biyu za su tattauna matsalolin da ke faruwa a yankunansu da ya shafi ilimi da muhalli da sauransu

- Advertisement -

Ana sa ran Shugaba Buhari ya dawo Najeriya a ranar Asabar mai zuwa

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: