Tsakanin Tiktok Da Facebook: tasirin bidiyo a kafafen sadarwa

Daga Mahmud Isa Yola

Alƙaluman bayanai sun yi nuni da cewa mafi akasarin masu amfani da social media sun karkata zuwa ga ƙirƙirowa da kuma kallon bidiyo. Wannan yasa a cikin ƙanƙanin lokaci, kafar sadarwa ta Tiktok tayi tasiri matuka musamman ga matasa. Tasirin Tiktok ya zama babban barazana ga Facebook, saboda a shekarar da ta gabata, kamfanin Facebook ta fiskanci tasgaro a ɓangaren ƙuɗaɗen shiga wanɗanda take samu daga masu amfani da manhajar, a daidai lokacin da adadin masu amfani da Tiktok sukayi tashin gwauron zabi.

Kamfanin Facebook ta fahimci wannan barazana tun a shekaru biyu da suka gabata, kuma tun a wannan lokaci ta fito da tsarin ‘Reels’ a Instagram. A wannan karon ma, yanzu Facebook ta bijiro da wannan tsari a manhajar ta.

‘Reels’ wani tsari ne na yin bidiyo wanda baida wani banbanci da Tiktok. Ma’ana mutum zai hada kilip-kilip na bidiyo masu sauti, ko kuma ya saka musu sauti da yake so. Dazarar mutum ya ɗaura bidiyon, mabiyan sa zasu gani, zasu iya ‘liking’ ko su tofa albarkacin bakin su a ƙarkashin bidiyon, ko kuma su aika shi zuwa ga abokan su.

- Advertisement -

Idan kana so ka ƙirƙiri ‘reels’ a Facebook, kawai zaka shiga alamar da take dauke da tambarin kafcen bidiyo, daga nan zai kaika kundin hotuna na wayar ka, inda zaka zabi bidiyo ko hoto da kake so ka dauka kayi amfani da su.

Facebook ta shirya nata samfurin na bidiyo wanda yake dauke da wasu abubuwa da Tiktok ba su da shi. Kamar misali, Facebook ‘reels’ zasu baka daman zaɓan waɗanda zasu kalli bidiyon ka, kamar yanda zaka zaɓi wadanda zasu kalli status naka na WhatsApp. Haka kuma zaka iya saka talla na wani kamfani a ƙasan bidiyon ka, wanda zasu biya ka idan mutane suka gani.

Babu shakka yanzu bidiyo shine abu mafi daukan hankali a social media. Wannan shi yasa Tiktok tayi fintinƙau, kuma ya sa Facebook ta fara shigo da wannan tsari. A saboda haka, masu amfani da kafar sadarwa saboda isar da sako, matukar suna so saƙon su yayi nisan zango, to sai su haɗa da irin waɗannan bidiyo.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: