Tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara: Ra’ayi na

Tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara: Raayi na.

Ko shakka babu, ba laifin da Mahdi yayi da har za a tsige shi a matsayin mataimakin gwamna, illa dai kin yadda da ya amince ya bi yarima ya sha kida. Ta daya bangaren, Gwamna Matawalle ya samu kan sa a halin zama da kunama a wando. Ya zamar masa wajibi ya san yadda zai yi ya kawar da ita, tun kafin ta dana masa.

Gwamna Rimi ya samu kan sa a irin wannan hali, a lokacin da ya raba gari da tafiyar Malam Aminu Kano, inda mataimakin sa Bibi Faruk yaki amincewa da wannan sabuwar hanya da gwamnan ya dauka, dalilin da ya sanya gwamnan ya kawar da shi, ya maye gurbin sa da Kwamishinan Gona, Alhaji Audu Dawakin Tofa. Hakan ta kara faruwa a Jihar Bauchi, tsakanin Gwamna Isa Yuguda da mataimakin sa, inda shi ma daga karshe mataimakin gwmnan ya rasa mukamin sa. Sai dai, rikicin da ya kunno kai tsakanin Shugaban Kasa Obasanjo da mataimakin sa Atiku Abubakar ya zo da bazata, inda Atikun yayi sauri ya garzaya kotu, tun kafin Obasanjo ya kare masa rurin numfashin sa a ofishin mataimakin shugaban kasa. Ya kuma yi sa’a kotu ta amince da cewa, yana da dama a shari’ance ya shiga duk kungiyar siyasar da yake so, ba tare da ya bar mukamin sa ba.

Gwamna Matawalle a ganina ya fahimci wannan tarihi, ya kuma san a shari’ance ba shi da wata hujja, amma kuma ya tuna bayan dara akwai wata cacar. Dan haka yayi amfani da karfin mulkin da siyasa ya kawar da mataimakin na sa. A fahimtata ta siyasa, kamar yadda masana suka tabbatar, siyasa mugun wasa ne, matukar baka iya makirci da sharri ba, zai wuya kayi nisa a cikin ta. Mahdi ya san da sanin cewa, daga ranar da yaki amincewa da ya bi gwaamna zuwa APC daga ranar kwanakin sa a ofishin mataimakin gwamna kayyadaddu ne. Na biyu ya san da cewa, ba shi da wata madafa a siyasance bayan karfin da mahaifin sa ke da shi. Wanda kuma bai taba wani tasirin ku zo ku gani ba a siyasar Jihar Zamfara ba. Babbar hanyar da za ta fisshe shi ita ce, ya jira a tsige shi, hakan zai sanya mutane su tausaya masa, wanda zai sanya ya kara farin jini.

- Advertisement -

Daga bangaren Gwamna Matawalle kuwa, ya lura da cewa, zaman Mahdi a gwamnatin sa, na da illoli da dama. Na farko dai ko ya aka samu wani sammatsi, to mataimakin sa shi zai dare kujerar. Na biyu zaman sa, na baiwa siyasar adawa ta PDP karin dama, kuma tunda yana gwamnati hakan zai iya bashi damar sanin wasu surruka na gwamnatin da ba zqta so yan adawa su sani ba. Na uku, tsige shi zai ba shi dama, ya kara dinke kyakkyawar alakar da suka kulla da bangaren APC dake karkashin jagorancin Yariman Bakura, kowa zai fahimci hakan, in aka lura da an dauko sabon mataimakin gwamnan ne daga cikin na hannun damar Yarima. Wannan a ganina da wasu dalilai suka sanya Gwamnatin APC a jihar Zamfara ta dau wannan mataki, da bisa ga zahirin gaskiya baiwa mutane da yawa dadi ba.

Ko dai ka kalli abin a matsayin zalunci ga Mahdi ko siyasa, ni dai a ganina, bangarorin biyu bukatar su ta biya. Farin jinin Mahdi dai ya karu, kuma mutane na masa kallon wani gwarzon dimokaradiya a Nigeria. Ko zai masa rana kamar yadda kunnen kashi ya yi wa Wamako rana a siyasar jihar Sakkwato, ko ba zai masa ba, wannan kuma sai zabe ya zo mun gani.

Babbar ribar da Matawalle ya ci a wannan dambarwa ita ce, ya yi amfani da damar, ya kara wa daben sa makuba, ta hanyar baiwa bangaren Yariman Bakura mukamiin mataimakin gwamna. A daidai lokacin da Kabiru Marafa da Abdulaziz Yari ke kara damarar yaki da bangaren gwamnan.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: