Uwargida ta kashe mijinta a Mararraban Nyaya saboda ya kara Aure

Daga Muryoyi

Hankula sun yi matukar tashi daren jiya Asabar a garin Mararrabar Nyaya bayan da wata mata ta kashe mijinta da wuka

Muryoyi ta ruwaito ma’auratan Atika da mijinta Ibrahim Ahmed (Mai Unguwa) sun samu yar hatsaniya a sakamakon karin aure da yayi inda zuciya ta dibi Atika ta dauko wuka ta caccaka wa mijin nata.

Lamarin, wanda ya auku a yankin Unguwar Yerima dake garin Mararrabar Abuja ta jihar Nasarawa, binciken farko ya nuna matar ta yanke wannan danyen hukuncin ne saboda tsabar kishin kara aure da mijin nata ya yi.

- Advertisement -

Mai Unguwa ya mutu nan take.

Ana sa ran za a yi jana’izar mamacin a safiyar yau Lahadi, inda ita kuma matar take tsare a hannun hukuma.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: