Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuVitamin D da hasken Rana

Vitamin D da hasken Rana

RA’AYIN: NAJIBULLAHI DANJUMA MUSA

 

VITAMIN D DA HASKEN RANA

Da yawa mutane idan Ina ganin comments dinsu na kanyi dariya sosai, domin a yadda su Dafta Abdul Suka kawo zancen sai ka dauka Ranar ce take kawo vitamin D.

MENENE VITAMIN D?

- Advertisement -

Vitamin D wani sinadarine da jiki yake buqata a adadi kadan domin samun damar zuqar sinadaran calcium da phosphate da kuma rikesu a cikin jini, wadanda suke taimakawa wajen ginawa da kuma qarfafar qashi.

A INA AKE SAMUN VITAMIN D??

Ana samun Vitamin D a adadi Mai yawa acikin abinci kamar tsokar fatty fish da kuma fish liver oils, sannan ana samunshi kadan a abinci kamar qwanduwar qwai, chizi, hantar rago ko ta saniya, kifi sardine, Solomon fish da kuma cod liver oil (cokali daya na cod liver oil Yana dauke da adadin Vitamin D din da jiki yake bukata a rana Daya har ninki uku). Sannan ana iya samunshi a abinci da akayi amfani da kimiyya aka dura vitamin D a cikin iri nasu suka fito suka girma tare da vitamin D din (wato fortified food) kamar su alkama ko shinkafa ko madara. Ana Kuma iya cire shi vitamin D din ayi shi a kwaya ko na ruwa (supplement).

Yawanci Vitamin D da muke ci acikin abinci baya kaiwa adadin da jiki yake bukata shiyasa Allah subhanahu wata’ala ya Samar da wata hanya da jikin mu zai iya tallafawa wajen cikasa abinda aka rasa na shi vitamin D ta hanyar amfani da hasken rana.

Haske Mai dauke da zafin rana (sun’s ultraviolet B) abinda yake Yi shine, dama jiki ya rigaya ya Samar da wani sinadari Mai suna 7-dehydrocholesterol, sai hasken rana yazo canja wannan sinadari zuwa “previtamin D3” daga previtamin D3 sai ya rikida (isomerization) zuwa vitamin D3.

Masana da yawa sun tafi akan cewa mafi kyawun inda za’a samu sinadarin vitamin D shine abinci wanda yake dauke da sinadarin vitamin D (musamman tsokar fatty fish da kuma fish liver oil) fiye da Samar dashi daga rana, domin rana tana haddasa illoli ga fata kamar su skin cancer.

Wadanda Kuma suke da duhun fata bincike ya nuna Suma hasken rana baya Isa inda sinadarin 7-dehydrocholesterol yake Wanda shine zai canza ya bada vitamin D. Haka wadanda suke aiki a inda babu rana, suma sukan samu qarancin wannan sinadari na vitamin D.

Shiyasa hanya mafi kyau na samunshi shine ta hanyar abinci.

NAJIBULLAHI DANJUMA MUSA
Public Health Nutritionist

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: