Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWai 'yan mata ba zasu samu miji ba sakamakon yawan sanya Niqabi...

Wai ‘yan mata ba zasu samu miji ba sakamakon yawan sanya Niqabi kuma zasu rasa sinadarin (vitamin D) idan suna yawan rufe jikinsu?

Daga Abubakar Umar Abubakar

Wata tace:
“wai ‘yan mata ba zasu samu miji ba; sakamakon yawan sanya Niqabi, wani kuma yace: wai zasu rasa sinadarin (vitamin D) idan suna yawan rufe jikinsu”.

Game da me magana ta farko, ga tambaya:
‘yan dirama ko yan film da suke rawa da Maza kuma suke kukan rashin mazan aure, su ma niqabin ne ya hana su samun Miji, koko ke da kike zaman zawarci kika tare a Facebook Niqabin ne ya hanaki Aure?!

Shi kuma wanda yace za’a rasa (vitamin D) ko wata tsiya can tasa.

- Advertisement -

Na farko dai idanma mun sallama cewa rufe jiki yana haifar da karancin sinadarin vitamin D, to shin Hijabi ko Niqabi da Mata suke sanyawa ko a kowane yanayine, shin Shari’a ta farrantawa me zaman gida da kuma me fita waje rufe ji?
A lokacin fita waje ne Shari’a ta Umarci Mace da Hijabi, kadai banda a cikin gida.
To bari mu yi gwari-gwari, mu dauka Mace ma’aikaciyace ko kuma daliba ce, zata fita tun safe karfe 8:00AM zata dawo karfe 4:00PM na yamma idan ta shiga gida zata cire Hijabinta da Niqabi, tunda a cikin gidanta take, wannan bai wadace ta ba sinadarin vitamin D din ba?

Abin nufi a cikin awa 24 na yini, Mata suna cire Hijabi na tsawon awa 14 ko 15 idan fita ta kama su, yayinda suke sanya shi a awa 7 ko 8 kadai, kenan dai lokutan cire Hijabi ko Niqabi su ne suka fi yawa akan sauran lokutan, koko dai har yanzu shi dan banza sinadarin vitamin D din yana bukatar sama da haka?!

Wannan fa idan mun sallama jadalan akan hakan kenan, alhali karyane babu wata Dirasa ko bincike sahihi da ya tabbatar wannan karyar.

Abu na biyu, daga cikin manufofin Shari’ar Musulunci guda biyar, akwai kare lafiya, wannan sune manufofin da duk wani hukunci na Shari’a baya fita daga cikinsu, Ubangiji shi ya wajabtawa Mata suturce jikinsu idan zasu fita, shi (subhanahu wata’ala) kuma me hikimane masani acikin duk tsarinsa don haka baya kuskure, tunda ya wajabtawa mata tufafi to ba zai yiwu ace zasu rasa lafiya ta sababinsa ba.

Abu na uku: Tajriba ta tsawon zamani bata nuna wannan labarin nasa yana da kamshin gaskiya ba, domin koda a coci-coci Mata masu ibadar Ruhubananci (Monastism) wato nuns, suna sanya tufafi irin na matan Musulmai, kuma kusan da shi suke kwana da yini musanman a zamanin da aka fi sani da (Dark Age) a Turai, idan gaskiyae da ya kamata mu samu rahoton irin wannan karyar a tarihance, musanman bayan juyin juya halin Faransa, da sai su rika cewa nuns basa samun sinadarin vitamin D, ko don suyi batanci ga matan coci.

وَلَوْ نَشَاءُ لَأَرَيْنَاكَهُمْ فَلَعَرَفْتَهُم بِسِيمَاهُمْ ۚ وَلَتَعْرِفَنَّهُمْ فِي لَحْنِ الْقَوْلِ ۚ وَاللَّهُ يَعْلَمُ أَعْمَالَكُمْ.

Allah ya raba mu da munafurcin aiki da magana.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: