Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWani mutum a Kaduna ya kashe makwafcinsa saboda bokitin ruwa

Wani mutum a Kaduna ya kashe makwafcinsa saboda bokitin ruwa

Daga Muryoyi

Wani matashi dan shekara 29 ya kashe makwafcinsa mai suna Liman Salisu a lokacinda rikici ya barke a tsakaninsu kan Bokitun ruwa.

Lauyan yan sanda mai shigar da kara, Inspector Chidi Leo ya shaidawa Kotu cewa rikici ya barke tsakanin Gado Yahaya mai sana’ar dinki da margayi Salisu Liman kuma dukkaninsu mazaunan garin Rigasa ne.

Muryoyi ta ruwaito Lauyan na cewa suna tsaka da fada ne sai zuciya ta kwashi Gado Yahaya inda ya shiga cikin gida ya dauko tabarya ya buga wa Liman Salisu akai kuma nan take ya yanke jiki ya fadi, kuma an dauke shi zuwa asibiti amma rai yayi halinsa a hanya.

- Advertisement -

Alkalin kotun Ibrahim Emmanuel ya bukaci a cigaba da tsare Gado Yahaya sannan ya daga sauraren karar zuwa ranar 9 ga watan Maris 2022

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: