Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWata Amarya a Bauchi ta kashe mijinta a wajen saduwa

Wata Amarya a Bauchi ta kashe mijinta a wajen saduwa

Daga Muryoyi

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama Amarya yar shekara 18 da ta dabawa Angonta wuka ya mutu a lokacinda ya kusanceta da nufin yin saduwar aure bayan ta tare a dakinsa.

Majiyar Muryoyi ta ruwaito Amaryar mai suna Salma ta shaidawa manema labarai cewa auren nasu bai kai sati biyu da daurawa ba, kuma da bakinta ta amsa wannan laifi da ake tuhumar ta da shi na kashe mijinta, wanda aka haɗa su auren zumunci tare.

Da take jawabi Salma ta bayyana cewa “An daura mana aure sai yazo zai yi iskanci dani sai nakiya hakan yasa ya mare ni sai ni kuma na dauki wuka na soka masa a kirji”

- Advertisement -

Kakakin yan sandan Bauchi ya ce haƙiƙa wannan lamari akwai abin duba a cikin sa, sai dai ba lallai a fahimci asalin maganar ba, tunda shi dai mijin nata ya riga ya mutu balle aji ta bakinsa kamar yanda akaji daga bakinta. Kodayake ya ce ta tabbatar masu cewa ita ta kashe shi ba tare da wani dalili ba in banda yadda tace cewa ya je kwanciyar aure da ita ne.

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: