Yadda aka daura Auren Jarumar fina-finai Aisha Tsamiya a boye 

Daga Muryoyi

Ana rade-radin an shammaci jama’a an daura Auren Jarumar FIM Aisha Tsamiya a safiyar jiya Juma’a sabanin yadda aka tsara gudanar da bikin tun a farko.

Majiya mai tushe ta shaidawa Muryoyi cewa ganin yadda jama’a sukayi dafifi yasa aka sauya komi game da tsarin auren “saboda tsaro domin wanda Jarumar zata Aura babban mutum ne kuma gashi ita ma Jarumar fim ce tana da jama’a”

Wani da yasan halin da ake ciki Ahmad Nagudu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

- Advertisement -

Daga ƙarshe dai an ɗaura auren jaruma A’isha Aliyu Tsamiya da Angon ta Alhaji Buba Abubakar a yau Juma’a – 25-02-2022

An ɗaura auren ne a yau kamar yadda aka tsara, amma an canja wajen ɗaurin Auren da lokacin da aka saka saboda dalilai na TSARO. Kasancewar mijin A’ishar babban mutum ne sananne, ita kuma fitacciyar jaruma ce wadda ke da ɗinbin masoya, wanda dalilin haka ya sa aka hango matsalar da muddin ana son kauce mata, to, dole a jirkita lamarin kamar yadda ya kasance, ba tare da an aiwatar kamar yadda aka tsara ba.

An dai ɗaura auren ne da safe ba kamar yadda ya ke da farko akan sai bayan Sallahr Juma’a ba. Haka nan an ɗaura ne a Masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa ba kamar yadda ya ke da farko akan a Masallacin Juma’a na Zarban da ke Ƴan Kaba ba.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: