Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba Su'Yan bangar Yarabawa "Amotekun" A Ondo Sun Kama 'Yan Ci-rani 63 A...

‘Yan bangar Yarabawa “Amotekun” A Ondo Sun Kama ‘Yan Ci-rani 63 A Maƙale Cikin Motar Shanu

Daga Ahmed Tijjani Ramalan

Jami’an hukumar tsaro ta Amotekun reshen Jihar Ondo, ta kama wata babbar mota a karamar hukumar Akure ta Arewa, ɗauke da maza kimanin 63 daga Arewacin Nijeriya.

Baya ga mutanen, an kuma ɗora wa motar shanu da raguna da babura, yayin da mutanen su ka ɓoye cikin dabbobin da baburan kamar yadda rahotan AID Multimedia Hausa ta rawaito.

Rahotanni sun ce, mutanen sun yi ikirarin sun taso daga Jihar Gombe, su na hanyar zuwa Legas kafin a taresu a kama su.

- Advertisement -

Direban motar mai suna Salisu Ahmed, ya ce su na kan hanyar su ta zuwa Legas ne, amma ya kasa yin bayani dangane da matasan da ke makale a motar.

Babban kwamandan Amotekun na jihar Ondo Cif Adetunji Adeleye, ya ce an kama mutanen ne, yayin da aka bincika motar aka gano ba dabobbi kadai da baburai da dauko ba, an cakudasu da mutane 63 da babura 10 masu rajista da sunan Yarbawa, da wasu 15 marasa rajista da kuma shanu 240.

Daman ba wannan ne karo na farko ba da ake muzgunawa Hausawa ba, yayin da suke zuwa ci-rani a kudancin Ƙasar Najeriya, idan mukai nazari da duba da yadda ‘yan kudancin ƙasar basu samun muzgunawa ko cin mutunci idan suka zo ci-rani a Arewacin ƙasar.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: