Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuZamu sayo jirage daga Turkiyya mu gama da yan bindigar da suka...

Zamu sayo jirage daga Turkiyya mu gama da yan bindigar da suka addabi yankin Arewa –inji El-Rufai

 

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce sun san inda ‘yan bindiga suke zaune amma “abin da ya hana a kai musu farmaki shekarun nan shi ne rashin samun damar a kira su ‘yan ta’adda kamar yadda aka yi wa Boko Haram… amma tun da yanzu kotun tarayya ta ce sojoji za su iya kashe su ba tare da an ce an kashe farar hula ba.” zasu yi wa yan bindigar kwaf daya.

Malam El-Rufai yace yanzu haka sun yi wani hadin guiwa shi da wasu gwamnoni a Arewa za su sayo jirage marasa matuka daga kasar Turkiyya domin magance matsalar ‘yan bindigar da ta addabi yankin.

- Advertisement -

Ya kara da cewa matsalar hare-haren ‘yan fashin daji na dada kamari a shiyyar kuma kasar ba ta da isassun jami’an tsaron da ke iya magance ta.

A cewar El-Rufai “Gwamnatin Turkiyya tana da wasu drone [jirage marasa matuka] masu daukar bam da rokoki, kuma mu gwamnatocin wadannan jihohi guda shida dama mun yi shiri za mu je Turkiyya mu zauna da shugabannin kamfanonin kasar mu sayo su [jirage marasa matuka], mu bai wa sojojin saman Najeriya su yi amfani da su,”

Gwamnan ya ce matsalar ta’addanci ta zarta duk yadda ake tunani kuma ‘yan bindiga suna samun makudan kudade don haka akwai bukatar a yi musu kwaf daya domin kawar da matsalar.

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: