Daga Muryoyi
Gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa duka masu rike da mukaman Gwamnati a jihar dake da sha’awar fitowa takara a zaben 2023 su ajiye aiki kamar yadda sabuwar doka ta umurta
Muryoyi ta ruwaito sanarwar hakan tana kunshe ne a cikin wata takarda da dauke da sanya hannun sakatare Gwamnatin jihar Kaduna, Balarabe Abbas da ya fitar yau Talata.
Ya ce an baiwa duk mai wani rike da mukamin Gwamnati wa’adin zuwa 3q ga watan Maris da muka ciki ya gabatar da takardar ajiye aiki wato ga Sakataren Gwamnatin jihar.
- Advertisement -