A bisa umurnin Buhari aka cire Mai Mala don haka ko ya dawo Najeriya zai dawo ne a matsayin Gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba –inji El-Rufai

Daga Muryoyi

 

A karshe dai ta tabbata cewa an sauke Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar APC,

 

Bayanin hakan ya fito fili ne daga bakin Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai inda kuma yace tuni Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi bayan cire gwamnan Yoben

 

A hirarsa da Channels TV a yau Talata Muryoyi ta ruwaito Gwamna El-Rufai na cewa Gwamnan Neja Sani Bello ne sabon shugaban APC na riko kuma tuni ya samu goyon bayan Buhari da kuma Gwamnonin APC 19.

 

 

- Advertisement -

Sannan ya ce Buhari ne ya ce a cire Gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

“Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi kuma aka aiwatar, yanzu gwamna Bello ne ya gaje shi,”

 

Don haka a cewar El-Rufai ko Mai Mala Buni wanda ba ya ƙasar a yanzu idan ya dawo Najeriya zai dawo ne a matsayin gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: