An kubutar da ɗan Ministan Sadarwa, Pantami jim kaɗan da sace shi
Daga Hausa Daily Times
Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da ɗan Ministan Sadarwar Najeriya Farfesa Isa Ali Pantami, a jihar Bauchi.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta samu labari, ɗan ya kubuta daga hannun masu garkuwar, an gano shi a wani shingen binciken jami’an tsaro da ke garin Dambam ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar Bauchi a ranar Juma’a.
- Advertisement -
Sai dai har izuwa yanzu babu cikkaken bayani kan adadin kuɗin da aka biya kafin masu garkuwar su sako ɗan ko kuwa jami’an tsaro ne suka kubutar da shi.
Yaron mai suna Alamin Isa Ali Pantami, yana zaune ne tare da kakarsa a Bauchi.
Da yake tabbatar da kubutar ɗan, ɗaya daga cikin ɗan uwan yaron ya ce, “Yanzu muka bar gidan ya dawo gida. An same shi ne a Dambam, inda masu garkuwa da shi suka ajiye shi. Sun ajiye shi a wani shingen bincike, daga nan aka dawo da shi gida.”
Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai musu rahoto kan lamarin ba.
Ya ce bayan an tuntube shi kan lamarin, ya tuntubi dukkan jami’an ‘yan sandan shiyya da ke cikin babban birnin jihar, amma suka ce ba a kai musu rahoto kan lamarin ba.