Daga Muryoyi
Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU reshen jami’ar ABU ta yi barzanar janye takardar shaidar kammala karatun “Certificate” din Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai
El-Rufai yayi karatu a ABU har ma ya fita da babban lamba mai daraja wato “First Class”
Sai dai a wata takarda da ke yawo a shafukan sada zumunta an ga yadda ASUU tayi taro da mambobinta a jiya Talata 2 ga watan Maris kan wani rikicin fili da ya hadasu da Gwamnatin jihar Kaduna,
- Advertisement -
ABU na zargin Gwamnatin Kaduna ta kwace ikon wani fili mallakin sashin karatun noma da kiwo na jami’ar ABU wato Agric Mando inda hukumar tsara birane da sufiyo ta jihar Kaduna KADGIS ta karbe ikon filin
Muryoyi ta ruwaito a cikin takardar bayan taron an ga ASUU din ta cimma matsaya guda Biyu, Na farko dai zata tura wakilanta su je filin wanda akace yana ta wajajen Mando
Sannan kuma ASUU ta duba yiuwar baiwa ABU shawarar ta janye takardar shaidar kammala karatu ta Elrufai saboda a cewarsu wasu abubuwa da yake yi basuyi kama da wanda yayi karatu a ABU ba