Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBuhari ya amince a kashe dala miliyan 8.5 domin kwaso ƴan Nijeriya...

Buhari ya amince a kashe dala miliyan 8.5 domin kwaso ƴan Nijeriya 5,000 dake Ukraine

Yaƙin Russia da Ukraine: Buhari ya amince da dala miliyan 8.5 domin kwaso ƴan Nijeriya su 5,000

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da dala miliyan 8.5 domin a gaggauta kwaso ƴan Nijeriya da su ka kai wajen 5,000 da yaƙin Russia da Ukraine ya rutsa da su.

Mafi yawan ƴan Nijeriya da yaƙin ya rutsa da su sun gudu zuwa Poland, Romania, Hungary da Slovakia.

Ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Zubairu Dada da Ministar Jin-ƙai, Sadiya Umar Faruk ne su ka baiyana hakan ga manema labarai jin kaɗan bayan an gama taron Majalisar Zartaswa na Mako-mako, FEC.

- Advertisement -

Dada ya ce an sahale fitar da maƙudan kuɗaɗen ne bayan da ministoci biyun su ka rubuta takarda ta haɗaka zuwa majalisar.

Ya baiyana cewa an baiwa kamfanin jiragen Air Peace da Max Air kwantaragi da su kawo jirage uku domin jigilar kwaso ƴan ƙasar.

Ministan ya ƙara da cewa waɗanda za a kwaso sun haɗa da mutane 940 da ga Romania, 150 da ga Slovakia, 350 kuma da ga Poland.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: